Oba Hameed Oyelude, Olowu na Kuta a karamar hukumar Ayedire ta jihar Osun, ya roki shugaban kasa Bola Tinubu da ya sake bude kan iyakar kasar da jamhuriyar Benin.
Oba Oyelude, wanda ya yi wannan roko a wata tattaunawa da ‘yan jarida a ranar Lahadi a fadarsa da ke Kuta, ya ce bude kan iyakar zai sauwaka wa ‘yan Najeriya matsalolin tattalin arziki.
“A lokacin da aka rufe iyakar Jamhuriyar Benin, gwamnatin tarayya tana kare tattalin arzikin kasar.
“Amma ina so in roki shugaban kasa ya duba yiwuwar sake bude kan iyaka don rage radadin ‘yan Najeriya,” in ji shi.
Ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da su yi hakuri da shugaban kasar, yana mai cewa yana nufin alheri ga kasar ta hanyar cire tallafin man fetur.
“Ribar cire tallafin man fetur na zuwa, amma watakila ba nan take ba. Don haka ne ya kamata mu yi hakuri da Shugaban kasa.
“Bari mu baiwa wannan gwamnati lokaci. Ba shakka za mu isa wurin,” basaraken ya roki.
Ya bukaci Gwamnatin Tarayya da kada ta dauki dukkan shawarwari da manufofin Asusun Ba da Lamuni na Duniya, IMF.
Sarkin ya ce duk da cewa babu laifi wajen sanya ra’ayoyi da manufofin IMF a cikin gida, amma dole ne a yi hakan ta hanyar da za ta dace da kasar.
“Akwai koma bayan tattalin arziki kuma kalubale ne da muke fuskanta, amma na yi imanin za mu shawo kan lamarin a matsayin kasa,” in ji shi.