fidelitybank

Tinubu ka bi mana kadin Ɗan mu ɗan shekara 6 – Iyayensa

Date:

Mahaifan wani yaro ɗan kimanin shekaru biyar da aka sace, sannan aka kashe a birnin Sakoto sun yi kira ga hukumomin tsaro na tarayyar Najeriya ƙungiyoyin kare hakkin bil adama, su bi musu kaɗin jinin ɗansu.

An dai sace yaron mai suna Ayman ne a daren ƙaramar sallah wato 29 da watan Maris a unguwarsu ta CBN Quarters Sokoto, sai bayan kwanaki 48 aka ga gawarsa cikin wani ramin ruwa wato Soakaway, a kusa da gidansu.

Mahaifin yaron Dakta Abubakar Hamza ya shaida wa BBC cewa an sace yaron ne bayan dawowa daga sallar la’asar, daga suka yi ta nema, sai wani ƙaramin yaro ya ce ai ya gan shi wasu sun saka shi cikin mota sun tafi da shi.

Ya ce bayan ƴan kwanaki sai wata mai suna Ummu ta ce masa ta son inda Ayman yake, wai an yi garkuwa da saurayin ƙawarta, wanda ya ce an tsare su tare da Ayman a yankin Kamba, ta kuma faɗa musu cewa za ta taimaka wajen dawo da yaron.

”To sai dai bayan da ta buƙaci kudi kuma muka ba ta sai maganar ta shirice, matar da riƙa yi mana gobe-gobe, har dai muka sanar wa hukumomi, suka kuma kamata, amma bayan bincike sun ce mana ƙarya take yi ba ta san inda Ayman yake ba”, in ji mahaifin yaron.

”Amma abin mamaki kwana biyu da suka wuce sai aka ganshi a cikin ramin ruwa (Soakaway)”.

Mahaifin yaron ya yi kira ga hukumomi su taimaka wajen bi masa kadin jinin ɗansa.

vgn news today 2021

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...

Isra’ila ta gano gawar ƴan ƙasarta

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta gano gawar ''yan...

Ma’aikatan wutar lantarki a Abuja sun fusata

Ma'aikatar kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja Electricity Distribution...

Ƴan Najeriya 147 da suka maƙale a Nijar sun dawo gida

Gwamnatin Najeriya ta tarɓi 'yan ƙasar 147 aka kwaso...

Alhazai Miliyan Ɗaya da Rabi ke tsayuwar Arfa

Dubun dubatar alhazai daga sassan duniya na hawan Arafa...

Sarkin Kano na 15 ya dakatar da yin hawan Sallah

Mai martaba Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado...

Maniyacin jihar Kano da yake kokarin zama Alhaji ya rasu a Saudiyya

Daya daga cikin alhazan jihar Kano, Shu’aibu Jibrin, an...

Tinubu ya bayar da tallafin Biliyan Biyu da Tirela 20 na Shinkafa ga al’ummar Mokwa

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya ce, shugaban ƙasar...

Gwamna Adeleke na Osun ya gana da Tinubu

Gwamnan jihar Osun Ademola Adeleke ya kai ziyara ga...

An samu gawar mutane 7 a ambaliyar Neja

Rahotonni na cewa masu aikin ceto sun zaƙulo gawar...
X whatsapp