Majalisar Koli kan Harkokin Shari’ar Musulunci a Najeriya, ta yi kira ga gwammnatin Tinubu da ta fito ta bayyana matsayarta kan rikicin da ake yi tsakanin Isra’ila da mayakan Falasdinawa.
Wannan na zuwa ne yayin da ƙasashe da dama ciki har da na Afrika ke ci gaba da nuna matsayarsu game da rikicin.
A wani taron manema labarai da ta yi yau a Abuja, majalisar ta kuma yi kira ga gwamnati da ɗaiɗaikun jama’a da su tattara kayan tallafi domin aika wa zuwa Gaza.


