fidelitybank

Tinubu ka bayyana kadarorin ka yau shekara guda kenan – SERAP

Date:

Ƙungiyar SERAP mai Fafutukar Yaƙi da cin Hanci SERAP, ta buƙaci shugaban ƙasar, Bola Tinubu ya yi amfani da bikin cikarsa shekara guda a kan mulki wajen wallafa takardun kadarorin da ya mallaka.

Cikin wata buɗaɗdiyar wasiƙa da ƙungiyar ta aike wa shugaban ƙasar, ta ce wannan dama ce da shugaban ƙasar zai nuna wa ‘yan ƙasar yadda yake son ci gaba dimokraɗiyya da nuna tsantseni da rashin rufa-rufa a gwamnatinsa.

Haka kuma ƙungiyar ta buƙaci shugaban ƙasar, ya umarci mataimakinsa da ministoci da gwamnonin jihohin ƙasar domin su wallafa nasu takardun kadarorin da suka mallaka.

SERAP ta ce: “Muna so ka wallafa takardun mallakar kadarorinka, sannan ka umarci sauran jami’an gwamnati su ma su yi haka, saboda hakan zai ƙarfafa samar da cikakken tsarin gwamnati maras rufa-rufa a duka matakai.”

“Yin abubuwa a bayyane ba tare da rufa-rufa ba, kamar yadda yake ƙunshe cikin takardun bayyana kadarori, zai inganta tsarin dimokraɗiyya tare da tsantseni a duka matakan gwamnati”, in ji SERAP.

Ƙungiyar ta kuma buƙaci shugaban ƙasar ya gaggauta bijiro da buƙatar yi wa kundin tsarin mulkin ƙasar kwaskwarima ta yadda za a saka dokar wallafa takardun mallakar kadarorin masu riƙe da muƙamai kafin su hau mulki da kuma idan suna kan mulki da bayan saukarsu.

hausa

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp