Kungiyar dalibai ta kasa NANS, ta yi kira ga gwamnatin Bola Tinubu da ta daidaita kanta da bukatun kungiyar kwadago.
A wata sanarwa da shugaban kungiyar Pedro Obi ya fitar a karshen makon da ya gabata, NANS ta tsaya tsayin daka da kungiyoyin kwadago a kan kiran da suka yi na karin albashi mafi karanci na kasa.
A yayin da ta ke bayyana matsalolin tattalin arziki da ake fuskanta a halin yanzu, kungiyar daliban ta lura cewa bukatar NLC ta dace.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Muna kira ga Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta mayar da martani ga halaltattun bukatun ma’aikatan Najeriya.
“Hakikan tattalin arzikin da ake ciki a halin yanzu sun lalata karfin sayayya na talakawan Najeriya. Hauhawar farashin kayayyaki, tsadar rayuwa, da kuma faduwar darajar Naira da ake ci gaba da yi, ya sa iyalai da dama ke da wuya su iya biyan bukatunsu na yau da kullum.”