Jam’iyun adawa sun soki matakin gwamnatin Tinubu na ƙara kudin wutar lantarki ga masu amfani da layin Band A da ake samun wuta tsawon sa’o’i 20.
Jam’iyar PDP da Labour sun ce matakin zai ƙara haifar da matsi ne ga ƴan ƙasar, babu wani abu bayan wannan.
Tun bayan sanar da matakin ƙarin kuɗin wutar da gwamnatin Najeriya ta yi, take fuskantar suka daga ɗaiɗaikun mutane ƙungiyoyi da kuma jam’iyyun siyasa na ‘yan adawa.
Sai dai gwamnatin Shugaba Tinubu ta ce da gwamnatin Najeriyar tana daukan dumar magaji da nishi ne..kasancewar dawainiyar ta fi karfinta…ga shi `yan kasa ba sa amfana daga tallafin naira sama da tiriliyan 3 da bangaren wutar ke lashewa a kowacce shekara. Amma da wannan za ta iya riƙa tsira da naira tiriliyan daya kowacce shekara da za ta iya karkatarwa zuwa ga ayyukan raya ƙasa.
A yammacin ranar Juma’a tsohon mataimakin shugaban Najeriya kuma ɗan takarar shugaban ƙasar a jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya wallafa a shafukansa na sa da zumunta cewa, “kamar yadda aka saba gwamnati ta ƙara yi wa talaka shaƙar mutuwa, ba tare da sanarwa ko ba da wa’adi ba, a kuma hakan matsi zai ƙara ga tattalin arziki”.
Irin dai wannan ra’ayi ne da jam’iyyar adawa ta Labour kamar yadda kakakinta Dr Yunusa Tanko ya yi ƙarin bayani.
“In gwamnati ba za ta iya ba ta kauce ta ba da wuri, amma abin babu tausayawa a ciki, dame za mu ji, arin kuɗin mai ko hauhawar farashin kayayyaki?”
Abdul’aziz Abdul’aziz na cikin masu taimakawa shugaban Najeriya kan harkokin yaɗa labarai, ya ce gwamnati ta tsinci kanta ne cikin tsaka mai wuya na kudaden tallafin da take biya a bangaren wutar lantarki.
“Abu ne da za ka iya cewa ya zama babu yanda za a yi, kuɗin da ake kashewa kan tallafin wuta kuɗaɗe ne masu yawa, kuma kamfanin da yake tafiyar da harkar yace babu kudinma a kasafin kudi na bana.
“A yanzu haka kamfanonin da suke rarraba wutar suna bin gwamnati makudan kudade na tallafin da ake biya. To ai babu ma’ana a ce ko da yaushe sai an kabo bashi za a biya wannan tallafi, kuma da za a karkatar da kudaden wani wuri da sun yi amfani.” in ji shi.
Abdul’aziz ya ƙara da cewa da sannu talakawan Najeriya za su yi farin ciki da wannan tsari a gaba. In ji BBC.