fidelitybank

Tinubu gyaran ƙasa za ka mayar da kai ba zaɓen 2027 ba – ACF

Date:

Ƙungiyar Tuntuɓar Juna ta Arewacin Najeriya, ta yi kira shugaba Tinubu da manyan muƙarraban gwamnatinsa da su mayar da hankali wajen ganin sun kyautata rayuwar ƴan Najeriya maimakon gangamin yaƙin neman a sake zaɓen Tinubu a 2027, inda a cewar ƙungiyar hakan ya yi wuri.

A wata sanarwa da kakakin ƙungiyar na ƙasa, Farfesa Tukur Muhammad-Baba ta taya Musulmi murnanr Babbar Sallah, ƙungiyar ta bayyana rashin jin daɗinta dangane da taɓarɓarewar tsaro da tsadar rayuwa da rashin wutar lantarki da matsalolin lafiya, ilimi da karyewar darajar Naira da tashin farashin kayan abinci.

Ƙungiyar ta kuma nuna takaicinta yadda duk da irin waɗannan ƙalubale amma jam’iyyar APC ta fi mayar da hankali kan gangamin yaƙin neman zaɓen Tinubun a 2027.

Idan dai ba a manta ba a watan da ya gabata ne dukkanin gwamnaonin jam’iyyar APC 22 a faɗin ƙasar suka amince da cewa Bola Tinubu ne ɗan takararsu a zaɓen 2027 mai zuwa, wani al’amari da ya janyo cece-kuce a Najeriya.

today nigeria news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Turji ya saki Mutane 32 bayan zaman sulhu

Shahararren shugaban ‘yan bindiga, Bello Turji, ya saki mutane...

ADC ta gargadi El’Rufa’i kan ruguza jam’iyyar

Shugaban jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a jihar Kaduna,...

An gindayawa Thomas Partey sharudan beli

An gindaya sharuddan belin tsohon dan wasan tsakiya na...

Fursunoni 37 na jiran zartas musu da hukuncin kisa a Bauchi

Fursunoni 37 da aka yanke wa hukuncin kisa bisa...

Kwamitin sulhu na MDD zai gana kan makomar ƴan Isra’ila da ke hannun Hamas

Kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya zai tattauna yau...

Sojoji sun kashe ‘yan Boko Haram 17 a Borno da Adamawa

Sojoji da ke aiki ƙarƙashin rundunar Operation Haɗin Kai...

Falana ya caccaki Tinubu kan salon tattalin arzikin Najeriya

Fitaccen lauyan nan mai kare haƙƙin bil adama, Femi...

Yahudawa sun yiwa Netanyahu tutsu kan mamaye Gaza

Ƴan'uwan Isra'ilawan da aka yi garkuwa da su a...

Cin zarafin Daliba ya sanya yin zanga-zanga a China

Zanga-zanga ta ɓarke a kudancin China sakamakon cin zarafin...

Tinubu ya baiwa ‘yan wasan kwallon kwando dala dubu 100 da filaye a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta karrama kungiyar kwallon kwando ta mata...

‘Yan siyasa na kara matsin lamba Jonathan ya fito takara a 2027 – Bashir

Tsohon mai taimaka wa tsohon shugaban kasa kan harkokin...

Gwamnati ta karbi tawagar ‘yan wasan kwallon kwando D’Tigress

Tawagar ƴan wasan ƙwallon kwando mata ta Najeriya ta...
X whatsapp