Tsohon gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi, ya ce Allah ya kawo shugaban kasa Bola Tinubu da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, domin ya warkar da kuma hada kan Najeriya.
Umahi ya bayyana hakan ne yayin da ya bayyana cewa shugaban kasa ne ke da hannu wajen bayyanar da Godswill Akapbio a matsayin shugaban majalisar dattawa.
Ya yi magana ne a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Arise a ranar Juma’a.
A cewar Umahi: “Allah ya kawo Tinubu da Shettima ne domin su warkar da al’umma su kuma hada kan ta, kuma ina so in yaba musu saboda maslahar kasar nan, mu sa al’umma a gaba.
“Duk masu kaunar kasar nan sun yi layi a bayan Akapbio a matsayin shugaban majalisar dattawa. PDP ta yi adawa da tikitin mu Musulmi da Musulmi, to me ya sa yanzu suke adawa da shugabancin Majalisar Dattawa Kirista?
“Na kasance daya daga cikin mutanen farko da suka fara nuna sha’awar tsayawa takarar shugabancin majalisar dattawa, kasancewar na kasance shugaban kungiyar gwamnonin kudu maso gabas, amma bai kamata a ga ina adawa da shugabana ba.”