Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima, za su fara biyan kudaden haraji a duk lokacin da suka shige ta kofar Toll Gate na filayen jiragen sama a kasar nan.
Hakan ya biyo bayan matakin da majalisar zartaswa ta tarayya, ta amince da cewa ba za a sake lamuntar kin biyan kudin harajin ba.
Hakan ya biyo bayan wata takarda da ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya gabatarwa majalisar, inda ya bayyana cewa gwamnati na asarar sama da kashi 82% na kudaden shigar da ya kamata ta samu daga e-tags da ke ba da damar yin amfani da kudaden.
Ya bayyana cewa tun da farko takardar ta ba da izini ga shugaban kasa da mataimakinsa ne kawai kafin Tinubu ya soke shi, kuma ya ba da umarnin a saka su duka a cikin wadanda dole ne su biya.
Keyamo, ya kuma ce, abun takaici ne ta yadda da dama attajirai masu matukar muhimmanci a kasar nan bas a biyan kiudin shigar na Toll Gate, wadanda ya kamata a ce su ke biyan kudaden.
Ministan ya ce talakawa ne kawai aka tuhume dole su ke biyan kudaden, lamarin da ya kamata a daina karba daga wajen su.
Tinubu da Shettima za su fara biyan kuɗin Toll Gate
Date: