Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da mataimakinsa Kassim Shettima, sun gana da gwamnonin jihohi 36, har da ministoci game da sabon albashi mafi karanci ga ma’aikata da sauran batutuwan da suka shafi tattalin arziki.
Shugaba Tinubu da gwamnoni sun gana a taron majalisar tattalin arziki ta kasa karo na 141 da aka gudanar a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ne ya jagoranci tattaunawar da gwamnoni da mataimakansu da kuma ministoci kafin isowar shugaban.
Taron ya zo ne kwanaki biyu bayan da majalisar zartaswar gwamnatin tarayya ta jinginar da batun mafi kankantar albashin domin ba da dama a kara yin tuntuba.
A ranar Laraba ne dai gwamnoni karkashin kungiyar gwamnoni ta kasa suka gana a Abuja, inda suka bai wa yan kasa tabbacin cewa tattaunawar da ake ci gaba da yi tsakanin gwamnati da bangarori masu zaman kansu da kuma kungiyar kwadago zai yi tasiri.
Ana sa ran shugaba Tinubu zai dauki mataki kan shawarar Naira dubu 62,000 da gwamnati ta bayar da kuma bukatar yan kwadago ta neman mafi karancin albashi ya zama Naira 250,000.