Shugaba Bola Tinubu da mai ɗakinsa, Remi Tinubu, sun karɓi bakwancin gwarzuwar kwallon kafa ta mata a Afrika Asisat Oshoala.
Tinubu da Remi, sun karɓi Asisat ne a gidansu da ke jihar Legas.
Oshoala ta sake lashe kyautar gwarzuwar kwallon kafa ta mata a Afrika na 2023, bayan ta doke waɗanda ta yi takara da su wanda suka haɗa da Thembi Kgatlana ‘yar kasar Afrika ta Kudu, wacce take taka leda a kungiyar Racing Louisville, da kuma Barbara Banda ‘yar kasar Zambia wadda ta ke taka leda a kungiyar Shanghai Shengli ta kasar sin.
Wannan shi ne karo na shida da Asisat Oshoala ta ke lashe kyautar, wadda take taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta mata.


