Mujallar Time ta Amurka ta sanya sunan zaɓaɓɓen shugaban Najeriya Asiwaju Bola Ahmed Tinubu cikin jerin mutum 100 masu ƙarfin faɗa a ji a duniya a 2023.
Cikin manyan shahararrun duniya da suka sanya akwai shugaban Amurka Joe Biden.
Karanta Wannan: Tinubu na huta wa a ƙasar waje kafin a rantsar da shi – APC
An kuma sanya sunan ‘yan wasan ƙungiyar PSG Lionel Messi da Kylian Mbappe daga bangaren wasanni.
Mujallar ta ce Tinubu ya cancanci shiga cikin jerin ne saboda “ya lashe zaɓe a ƙasar da ta fi kowacce yawan jama’a a najhiyar Afrika wanda hakan ba abu bane mai sauƙi. Kuma ya kwashe kimanin shekara 20 yana ta shirya yadda zai kai ga wannan matsayi.