Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, ya ce ya buƙaci lauyoyinsa su daukaka ƙara zuwa Kotun Koli.
Yayin da yake jawabi a taron manema labarai da jam’iyyarsa ta shirya kan hukuncin kotun sauraron ƙorafin zaɓe, Atiku ya ce “faɗan bai ƙare ba”.
Atiku ya ce ya je kotun ne bisa imanin samnun adalci. “A tarihin siyasata ina da yaƙini kan ɓangaren shari’ar ƙasarmu,” in ji shi.
“Tabbas ni ba baƙo ba ne a fannin shari’a, kuma zan iya cewa na san yadda tsarin ke aiki. Na daɗe ina gwagwarmaya a tsawon shekarun da na shafe a matsayin ɗan siyasa, kuma ina ganin zan iya dogara da ɓangaren shari’a wajen neman adalci.”
A ranar Laraba ne kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓen shugaban ƙasa ta yi watsi da ƙarar da Atiku da PDP da wasu jam’iyyun adawa suka shigar suna ƙalubalantar nasarar Shugaba Tinubu na APC.


