Fadar shugaban kasa ta ce, shugaban kasa Bola Tinubu, bai nemi Yemi Cardoso ya yi murabus daga mukaminsa na gwamnan babban bankin Najeriya CBN ba.
Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan yada labarai, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, inda ya karyata rahotannin da ke cewa Tinubu ya ba da umarnin murabus din Cardoso.
A cikin sakon da ya fitar ta hannun jami’insa na X ranar Talata, kakakin shugaban ya bayyana rahoton a matsayin tarin karya.
“Duk karya ne. Shugaba Tinubu bai nemi Yemi Cardoso ya yi murabus ba,” in ji Onanuga.
Rahoton ya bayyana cewa, shugaba Tinubu ya bayar da umarnin ne ga Cardoso kafin ya tashi zuwa kasar Sin, duk da kokarin da shugabannin Yarbawa masu fada a ji na ganin ya ci gaba da rike shi.
Ku tuna cewa Gwamnan CBN ya sha suka kan gazawar sa wajen magance kalubalen tattalin arzikin da ake fama da shi da kuma daidaita darajar Naira.