fidelitybank

Tinubu ba zai taba goyon baya a wawure dukiyar al’umma ba – Adeleke

Date:

Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya tabbatar da cewa shugaban kasa Bola Tinubu ba zai taba goyon bayan a wawure dukiyar al’umma ba.

Ya yi magana ne a matsayin martani ga zargin da jam’iyyar APC ta Osun ta yi game da wata farar takarda da aka fitar kwanan nan.

Shugabannin jam’iyyar APC a jihar sun yi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu da jami’an tsaro da su taimaka wajen ceto jihar daga mulkin kama karya na Gwamna Adeleke da jam’iyyarsa ta PDP mai mulki.

Gwamnatin jihar Osun a ranar 18 ga watan Junairu, 2024, ta fitar da wata farar takarda akan sarakunan gargajiya da kuma karbo kadarorin al’umma da ake zargin wasu masu rike da mukamai na siyasa a karkashin gwamnatin Adegboyega Oyetola.

A cewar Gwamna Adeleke a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Olawale Rasheed ya fitar, “Shugaban kasa a kodayaushe ya yaba masa kan yadda ya kawar da duk wata matsala da ya hadu da shi a Osun, yayin da ya kuma jaddada cewa shugaba Tinubu ya kyamaci sace dukiyar al’umma.

“Na sha yin mu’amala da Shugaba Tinubu, kuma na san ya yaba da kokarin da na yi wajen tsaftace dimbin matsalolin da na fuskanta a Osun.

“Daga ayyukan shugaban kasa, ya nuna cewa shi mutum ne mai bin ka’ida, don haka ba zai taba goyon bayan wawure dukiyar jama’a ba. Yanzu abin takaici ne yadda Osun APC ke nuna ayyukan da suka saba wa salon mulkin Shugaban kasa

“Moreso, a farkon gwamnatinmu, na kafa kwamitin kwato kadarori, tare da sanar da mafi yawan wadanda ke da kadarorin gwamnati kan bukatar dawo da su.

“Yanzu shi ne rahoton kwamitin da nake aiki da shi kamar yadda mutanen kirki na jihar suka bukata.”

Gwamna Adeleke, yayin da yake tabbatar da cewa ya na mulkin jihar ne ba tare da bangaranci ba, ya bayyana cewa bai jawo wani abokin adawar siyasa ga hukumomin yaki da cin hanci da rashawa ba ko da akwai wasu dalilai na yin hakan.

A yayin da yake kira ga wadanda aka nada a gwamnatin da ta gabata a jihar da su mayar da dukkan kadarorin gwamnati da ke hannunsu, Adeleke ya yi gargadin cewa gwamnatinsa ba za ta bari a kwato duk kadarorin gwamnati da aka wawashe ba.

nnnnews

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Kotu ta bayar da umarni a kashe Matashi ɗan shekara 23 a Kano

Babbar kotun jihar Kano mai lamba 23 ƙarƙashin mai...

Iran ta na ci gaba da luguden makami a kan Isra’ila

Iran ta ci gaba da lugudan wuta a Isra'ila...

An yi sulhu da shugabannin ƴan Bindiga a Katsina

Wasu al'ummar Katsina, sun yi sulhu da wasu shugabannin...

Za a fuskanci ambaliya a wasu jihohin – NIMET

Hukumar kula da yanayi ta NiMet, ta ce akwai...

Za mu mayar wa da Isra’ila martani mai tsanani – Iran

Shugaban ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya yi alwashin mayar...

Ba za mu taɓa barin Iran ta ƙera makamai masu linzami ba – Isra’ila

Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya ce burin ƙasarsa shi...

Isra’ila ta buga gangar yaƙi – Iran

Jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya ce...

Iran ta na cigaba da luguden makami mai Linzami cikin Isra’ila

Ana ci gaba da zaman dar-dar a Isra'ila yayin...

Alhazan Najeriya sun fara dawo wa daga ƙasar Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta sanar da isowar...

Sojoji sun kama ɗan kasar China da zargin kai wa ƴan Boko Haram kayayyaki

Rundunar sojojin ƙasar nan ta kama wani dan kasar...

Isra’ila ta tsokano tsuliyar Dodo – Iran

Jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei ya ce...

Da sani na Isra’ila ta kai hari Iran – Trump

Shugaban Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa, yana sane...
X whatsapp