Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, ya mayar da martani kan shaidar takardun dan takarar shugaban kasa a jamâiyyar APC, Bola Tinubu, inda ya ce, idan har kundin tsarin hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ya kasance mai inganci kuma ya na rumbun ajiyarta, dan takarar baya bukatar sabon gabatar da takardunsa.
Gwamnan ya bayyana haka ne bayan ziyarar godiya da ya kai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari kan amincewa da gudanar da bikin ranar sojoji a Owerri, yana mai cewa. hakan zai karfafa matakan da aka dauka a kasa na dakile âyan fashi da rashin tsaro a yankin da kuma aike da sako mai karfi ga masu aikata laifuka.
Tinubu ya nuna a cikin takardar rantsuwa da ya mika wa hukumar zaben cewa, bai halarci makarantun firamare da sakandare ba.
Sai dai tsohon gwamnan na Legas ya yi ikirarin cewa yana da digiri biyu a jamiâoâin Amurka guda biyu, inda ya ce wasu da ba a san ko su wanene ba ne suka sace su a lokacin mulkin soja na shekarun 1990.