fidelitybank

Tinubu ba na bukatar mukami a gwamnatin ka – El-Rufa’i

Date:

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El Rufa’i ya ce ya faɗa wa shugaba Bola Tinubu cewa ba ya son wani muƙami a gwamnatinsa.

El Rufa’i ya bayyana haka ne a shafinsa na X yayin martani ga babban mai taimaka wa shugaban ƙasa kan sadarwar tsare-tsaren gwamnati, Daniel Bwala, wanda ya ce El Rufa’i ya ji tsoron Allah bayan da ya fito fili ya caccaki jam’iyyar APC da kuma kiran ta mai mulkin da ta “sauka daga aƙidun dimkoraɗiyya da aka kafa ta a kai”.

“Na faɗa wa Tinubu ƙarara cewa ba na buƙatar kowane irin muƙami a gwamnatinsa,” in ji El Rufa’i.

Ya ce yana mamakin irin yadda Daniel Bwala da takwarorinsa da suka koma jam’iyyar APC a baya-bayan nan ke ta yayata batun cewa an hana shi muƙami, abin da ya ce ba ya so tun da farko.

“Ina mayar maka da martani ne saboda ina tunanin cewa kai mai fahimta ne wanda ke neman aiki, ba irin wasu mutane ba.

“Ku mutane ne da ke karɓar albashi kowane wata don ku fara fitowa a shafukan sada zumunta wajen kare kowane irin abu da gwamnatin Asiwaju ta yi ko kuma ta ƙasa yi,” in ji tsohon gwamnan na Kaduna.

Ya ce ko da ace yana cikin gwamnatin shugaba Tinubu – babu abin da zai hana shi furta kalaman da ya yi kan abin da ke faruwa a jam’iyyar da ya ce su suka kirkiro – har ma da kawo gwamnati mai ci.

daily post today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp