Tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Abdulsalami Abubakar, ya bayyana rashin gamsuwarsa da biyan mafi karancin albashi na N30,000, inda ya bayyana cewa ba za a amince da shi a halin da ake ciki a Najeriya ba.
Abdulsalami ya yi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu da ya yi la’akari da kara albashi mafi karanci, domin a ganinsa cewa N30,000 ba za ta iya haifar da ci gaban dan Adam mai ma’ana a ko’ina a duniya ba.
Tsohon shugaban kasar ya yi wannan jawabi ne a Jalingo, babban birnin jihar Taraba, Laraba, a lokacin da yake gabatar da jawabi a wajen taron samar da zaman lafiya, hadin kai da sulhu, wanda kwamitin zaman lafiya mai zaman kansa na Taraba ya shirya.
Shugaban sakatariyar cibiyar Kukah da kwamitin zaman lafiya na kasa Rev Fr Atah Bakindo ya wakilce shi, ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi amfani da albarkatun da ke yankunansu domin inganta rayuwarsu.
“Ina so in roki shugaban Najeriya cewa mafi karancin albashi na N30,000 ba zai iya daukar ‘yan Najeriya a ko’ina ba. Ba a yarda da shi a ko’ina cikin duniya, kuma ba zai iya haɓaka kowa ba; akwai bukatar a kara albashi cikin gaggawa domin ci gaban mu.
“Ina so in yi kira ga al’ummar Jihar Taraba da su sasanta kowane irin bambance-bambancen da ya haifar da rikici da rashin hadin kai. Ba za ku iya amfani da wani ci gaba ba idan ba ku cikin zaman lafiya da haɗin kai. Kuna da sa’a don samun albarkatun kasa; zaman lafiya da hadin kai ne kawai ginshikin ci gaba,” inji shi.


