fidelitybank

Tinubu a na fama da yunwa a Gwamnatin ka – LP

Date:

Jam’iyyar Labour Party, LP, ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta ba da fifiko wajen inganta rayuwar ‘yan Nijeriya.

Sakataren jam’iyyar na kasa Umar Farouk Ibrahim ne ya yi wannan kiran a matsayin martani ga takun saka da aka samu a kasar nan.

An samu turmutsutsu a Oyo, Anambra, da kuma babban birnin tarayya, FCT, inda sama da mutane 50, ciki har da kananan yara suka mutu a lokacin rabon kayan abinci na karshen shekara.

A cikin wata sanarwa a ranar Litinin, sakataren LP, ya ce ‘yan Najeriya sun yanke shawarar yin kasada don ci gaba da rayuwa sakamakon tsadar rayuwa a kasar.

“Batun magana ita ce, akwai yunwa a cikin ƙasa. Talauci ne kawai ya sanya wasu ‘yan Najeriya ke diban mai a wuraren da hatsarin ya rutsa da su, lamarin da ya janyo tashin gobarar da ta janyo asarar rayuka.

“Wannan ya faru sau da yawa a cikin shekarar da ta gabata.

“Babban dalilin da ya sa mutane ke aikata laifuka shi ne yunwa. ‘Yan Najeriya miliyoyi sun fuskanci yunwa sakamakon wasu dalilai kamar hauhawar farashin kayayyaki da rashin tafiyar da tattalin arziki.

“Sake fasalin tattalin arzikin gwamnatin Tinubu ya jawo wa ‘yan Nijeriya wahalhalun da ba za a iya mantawa da su ba. Yunwa tana rikidewa zuwa annoba, kuma ba mutane da yawa ba ne za su iya tsira daga wannan yanayin,” in ji shi.

A cewarsa, ya kamata a yi amfani da albarkatun kasa wajen inganta jin dadin ‘yan kasar.

Ibrahim ya kara da cewa babu wani abu na zahiri da gwamnati ta yi domin magance matsalar yunwa da kuma duba irin talaucin da ake fama da shi a Najeriya, yana mai jaddada cewa dole ne gwamnati ta tashi tsaye ta hada ayyukanta.

legits news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...

Isra’ila ta gano gawar ƴan ƙasarta

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta gano gawar ''yan...

Ma’aikatan wutar lantarki a Abuja sun fusata

Ma'aikatar kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja Electricity Distribution...

Ƴan Najeriya 147 da suka maƙale a Nijar sun dawo gida

Gwamnatin Najeriya ta tarɓi 'yan ƙasar 147 aka kwaso...

Alhazai Miliyan Ɗaya da Rabi ke tsayuwar Arfa

Dubun dubatar alhazai daga sassan duniya na hawan Arafa...

Sarkin Kano na 15 ya dakatar da yin hawan Sallah

Mai martaba Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado...

Maniyacin jihar Kano da yake kokarin zama Alhaji ya rasu a Saudiyya

Daya daga cikin alhazan jihar Kano, Shu’aibu Jibrin, an...

Tinubu ya bayar da tallafin Biliyan Biyu da Tirela 20 na Shinkafa ga al’ummar Mokwa

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya ce, shugaban ƙasar...

Gwamna Adeleke na Osun ya gana da Tinubu

Gwamnan jihar Osun Ademola Adeleke ya kai ziyara ga...

An samu gawar mutane 7 a ambaliyar Neja

Rahotonni na cewa masu aikin ceto sun zaƙulo gawar...
X whatsapp