fidelitybank

Tinibu ya ƙaddamar da rabon tallafin kuɗi ga Magidanta miliyan 15

Date:

Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya kaddamar da shirin ba da tallafin kuɗi ga magidanta miliyan 15, wanda hakan na cikin manufofinsa da aka yi wa laƙabi da ‘kyakkyawan fata’.

Tinubu ya kaddamar da shirin ne a yau Talata a bikin ranar kawo karshen talauci ta duniya, wanda aka gudanar a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Tinubu ya samu wakilcin sakataren gwamnatin tarayya, George Akume yayin kaddamar da shirin.

A jawabinsa na bikin samun ƴancin kai a ranar 1 ga watan Oktoban 2023, shugaban ya sanar da cewa shirin ba da tallafin kuɗin, zai fi mayar da hankali kan taimakawa marasa galihu.

Magidantan da iyalansu sun kai yawan ƴan Najeriya miliyan 62, a cewar ministar ba da agaji, Betta Edu.

Ta ce za a bai wa kowane magidantci naira 25,000 har na tsawon wata uku, wanda ya kai naira 75,000.

Ministar ta kuma ce nan ba da jimawa ba, za a kaddamar da wani tsarin ba da tallafi mai suna ‘Iya Loja Funds’ wanda zai samarwa masu ƙananan sana’o’i bashin naira 50,000 kowanne.

Waɗanda suka halarci bikin sun haɗa da ministar ma’aikatar ba da agaji rage talauci Dr Betta Edu, ministan kuɗi, Wale Edun, wakilin bankin duniya na ƙasashe, Shubham Chaudhuri, shugaban ba da agaji na Majalisar Ɗinkin Duniya a Najeriya, Matthias Schmale da sauran manyan baki.

nigeria news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp