fidelitybank

Tilas Ukraine ta amince cewa yankin Crimea mallakin Rasha ne – Rasha

Date:

Rasha ta ce za ta iya kawo karshen ayyukan soji da ta ke yi “a duk lokacin da ta so” idan Ukraine ta cimma wasu sharuddan da Rashar ta gindaya.

Kakakin Fadar Kremlin Dmitry Peskov ya ce, tilas Ukraine ta amince cewa yankin Crimea mallakin Rasha ne, kuma Donetsk da Luhansk kasashe masu zaman kansu ne.

Baya ga wadannan, Peskov ya kuma ce tilas Ukraine ta sauya tsarin mulkinta kuma ta yi watsi da niyyar shiga wata kungiya (a misali Nato).

Ya kara da cewa Rasha za ta kammala tsaftace Ukraine, kuma sai bayan an biya dukkan wadannan bukatun ne “ayyukan sojin” da dakarunta ke yi za su kawo karshe “nan take”.

Kakakin Fadar Kremlin din ya nanata cewa Rasha ba ta da niyyar mallake kasar Ukraine fiye da wanda ta yi a yanzu.

Rasha ta kwace yankin Crimea ne a watan Maris din 2014, kuma bayan wasu makonni ta goyi bayan ‘yan awaren da ke kokarin ballewa daga a yankunan Donetsk da Luhansk na gabashin Ukraine.

punch news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp