Kamfanin TikTok na China ya ce, zai dau matakin shari’a domin kalubalantar haramta amfani da shafin da jihar Montana ta Amurka ta yi.
A karar da ya shigar, TikTok ya ce Jihar Montana ta saba dokoki da aka cimma bayan kwaskwarima a kundin tsarin Amurka, ta hanyar tauye hakkin fadin albarakcin baki.
Dokar haramta amfani da shafin wadda gwamnan jihar Greg Gianforte ya sanya wa hannu ranar Laraba za ta fara aiki ranar 1 ga watan Janairu na 2024.
Dokar ta tanadi cin tarar kamfanin na TikTok idan ya ci gaba da gudanar da ayyukansa a jihar da kuma hana mutane sauke manhajar a wayoyinsu.
‘Yan majalisa a Amurka dai na ganin gwamnatin China za ta iya amfani da wannan manhaja wajen kutse da tattara bayanan sirrin kasar ta Amurka.
Kamfanin na TikTok ya musanta alaka ko mika bayanan masu amfani da manhajar ga gwamnatin China.