Wani matashi mai matsakaicin shekaru wanda har yanzu ba a bayyana sunan shi ba ya mutu a bayan da motar ɗaukar yashi ta talitse shi a Owode-Ede ranar Juma’a.
Hatsarin ya afku ne a daidai lokacin da mai tattaki ya yi yunkurin tsallaka titin Gbongan zuwa Osogbo da ke Owode-Ede mai cike da cunkoson jama’a a lokacin da mai shigowa ya rutsa da shi tare da take shi.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa, sakamakon hatsarin, an samu cunkoson ababen hawa na wani dan lokaci da kuma rudani a kasuwar Owode-Ede.
Kazalika sun bayyana cewa direban da mai taimaka masa sa sun gudu ne bayan da suka hango mutanen da ke cunkoso a wurin da hatsarin ya afku.
Kwamandan hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC) reshen jihar Osun, Paul Okpe, ya tabbatar da faruwar hatsarin, ya bayyana cewa an samu asarar rayuka.
Okpe ya bayyana cewa an ajiye gawar mai tafiya a wani dakin ajiyar gawa da mutanensa suka yi.
“An yi hatsari a Owode-Ede. Wani direban tipper ya ci karo da wani mai tafiya a ƙasa wanda ya yi ƙoƙarin tsallaka titin. Da sauri tawagarmu ta garzaya yankin inda suka kwashe gawar zuwa dakin ajiye gawa a jihar.
“Mun samu labarin cewa direban tipper ya gudu. Ina tsammanin da ya ga jama’a sun taru, sai ya dauka suna so ne su yi masa zanga-zanga, suka gudu da mai taimaka masa,” inji shi