Majalisar dokokin Thailand ta tabbatar da Paetongtarn Shinawat, ƴar tsohon jagoran ƙasar Thaksin Shinawat, a matsayin firaminista.
Ƴar shekaru talatin da bakwai ta zama shugabar gwamnati mafi karancin shekaru a Thailand.
Ta maye gurbin Setta Tawisin (Srettha Thavisin) da kotun tsarin mulkin Ƙasar ta kora a farkon makon nan.
Ms Paetongtarn za ta fuskanci babban Ƙalubale na farfaɗo da tattalin arzikin da ya durƙushe da kuma barazanar juyin mulkin sojoji waɗanda suka hambarar da gwamnatoci huɗu na baya ƙarkashin jagorancin danginta.
Sabuwar firaiministar ta ce tana fatan zata zamo abin alfahari ga jama’a, sannan tana neman goyon bayan al’ummar ƙasar domin hakan ne zai ƙarfafa mata gwiwa da kuma bata damar yin abin da ya kamata.
Ta ce,” Ni ba ƙwararriya bace, to amma zan yi iya kacin baƙin ƙokari na wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyana.”