Ƙasar Thailand na zaman makoki bayan kashe aƙalla mutum talatin da takwas waɗanda akasarinsu yara ne waɗanda aka caccaka wa wuƙa da harbi da bindiga a wata makarantar renon yara a jiya Alhamis.
An yi ƙasa da tutocin ƙasar sannan kuma sarkin ƙasar da firaiminista duk za su kai ziyara ga iyalan waɗanda aka kashen a garin Utthai Sawan.
Ƴan sanda sun ce yara 23 da aka kashen dukkansu ba wanda ya wuce shekara biyar haka kuma maharin ya kashe har da wasu malaman makarantar.
Wanda ya kai harin tsohon ɗan sanda ne wanda ya fuskanci tuhume-tuhumen miyagun ƙwayoyi.
Ƴan sanda sun ce bayan aika-aikar da mutumin ya yi, sai ya tafi gida ya kashe matarsa da ɗansa sa’annan ya harbe kansa.