Ƙasashen Thailand da Cambodia sun amince da tsagaita wuta ba tare da ɓata lokaci ba kuma ba tare da wani sharaɗi ba” bayan kwana biyar na faɗa a kan iyakar ƙasashen biyu.
Faɗar ta yi sanadin mutuwar mutum aƙalla 33 tare da raba dubban mutane da muhallansu.
“Wannan babban mataki ne na farko wajen rage rikici da dawo da zaman lafiya da tsaro,” in ji firaministan Malaysia, Anwar Ibrahim, yayin da yake sanar da dakatar da faɗa yana mai cewa an cimma matsaya cewa za a daina faɗa daga ƙarfe 12 na dare.
A farko, Thailand ta ƙi amincewa da tayin shiga tsakani da Anwar ya bayar, sai dai ta amince daga bisani bayan shugaban Amurka Donald Trump ya ce ba za a cigaba da tattaunawar haraji ba har sai “an daina faɗa”.
Tashin hankali a kan tsohuwar takaddamar kan iyaka ya ƙara ƙamari a watan Mayu bayan wani sojan Cambodia ya mutu a wata arangama.
Daga bisani kuma Thailand ta sanya takunkumi ga ‘yan ƙasa da yawon bude ido daga shiga Cambodia ta hanyar ƙasa, yayin da Cambodia ta haramta shigo da wasu kayayyaki daga Thailand.
Lamarin ya ƙara ta’azzara a makon da ya gabata, bayan wani soja dan Thailand ya rasa ƙafarsa a fashewar bam.