Rahotanni na cewa mai horas da Manchester United, Erik ten Hag, zai rage albashi mai tsoka, har idan ya ci gaba da zama a kungiyar bayan karshen kakar wasa ta bana.
ESPN ta ba da rahoton cewa, Ten Hag zai rage albashi mai tsoka na kashi 25 a Old Trafford, sakamakon rashin nasarar da kungiyar ta yi na samun cancantar shiga gasar zakarun Turai.
Dan kasar Holland, wanda ya rattaba hannu kan kwantiragin shekaru uku da kungiyar, bayan ya koma Ajax a watan Mayun 2022, yana fuskantar matsin lamba tare da kungiyar tana matsayi na bakwai a kan teburi.
United tana matsayi na farko da maki 16.
Sai dai kawo yanzu, ‘Yan takarar masu son maye gurbin Ten Hag, sun hada da Gareth Southgate na Ingila, Thomas Tuchel na Bayern Munich, Roberto De Zerbi na Brighton, Thomas Frank na Brentford, da kuma Gary O’Neil na Wolves.