Kocin Manchester United Erik ten Hag, na shirin siyan dan wasan tsakiya na Juventus Adrien Rabiot a matsayin kyauta a wannan bazarar.
Rabiot dai zai kare kwantiraginsa da Juventus a watan Yuni.
Juventus ta amince da kudi da Man United kan Rabiot a bazarar da ta gabata, amma bukatun albashin da ya ke nema ya gamu da matsala.
Daga karshe Man United ta dauki Casemiro daga Real Madrid a maimakon haka, yayin da Christian Eriksen kuma ya zo daga Brentford.
Duk da haka, Ten Hag yana da sha’awar Rabiot, kuma a cewar L’Equipe, dan kasar Holland ya yi magana da dan wasan na Faransa game da komawa Old Trafford.
Yayin da yarjejeniyar Rabiot a Juventus za ta kare a wata mai zuwa, Man United za ta iya siyan shi kyauta a wannan bazarar kuma za ta fi son biyan bukatar albashin sa saboda ba za su saka kudi ba.