fidelitybank

Tchiani ya zargi Najeriya, Faransa, China da Amurka wajen cutar da Nijar

Date:

Shugaban sojin Nijar, Janar Abdourahmane Tchiani, ya zargi Najeriya da haɗa baki da Faransa da China da Amurka wajen ɗaukar nauyin ayyukan ta’addanci a ƙasarsa.

A cikin wani jawabi na awa uku da aka watsa kai tsaye a gidan talabijin na Radio-Télévision du Niger (RTN) a ƙarshen mako, Tchiani ya yi magana da harshen Hausa, Zabarma da Faransanci, inda ya zargi Najeriya da Jamhuriyar Benin da Faransa da China da Aljeriya da Amurka da kokarin dagula ko cutar Nijar da sauran ƙasashen da ke cikin ƙawancen AES.

Wannan shi ne karo na biyu da Tchiani ke zargin Najeriya a yayin wata hira da ya yi ta ranar Kirsimeti a bara, inda ya ce Faransa na haɗa baki da ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya a yankin tafkin Chadi domin lalata tsaron Nijar, tare da sanin Najeriya.

Tchiani ya ƙara da cewa an gudanar da wata ganawa a ɓoye a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya a watan Disamba na shekarar 2024 domin tsara yadda za a afka wa Nijar.

Haka zalika, Tchiani ya ce a watan Janairu 2025, wakilan Benin da Côte d’Ivoire da wasu ƙasashen Yammacin Afirka sun sake haɗuwa a Abuja domin sake nazarin dabarunsu na cutar da Nijar, amma suka gamu da cikas bayan shirin ya ci tura.

Waɗannan zarge-zargen sun biyo bayan hare-haren da ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya suka kai a yankunan Tahoua da Dosso, inda aka kashe sama da sojoji 100, lamarin da ya tayar da hankalin jama’ar Nijar.

Tuni gwamnatin Najeriya ta mayar da martani dangane da wannan sabon zargi, inda ta karyata iƙirarin gaba daya tare da bayyana shi a matsayin maras tushe ko makama.

Masu fashin baƙi dai na alaƙanta irin waɗannan zarge-zarge da shugaban sojin ya yi da ƙoƙarin wanke kansa da kuma burge al’ummarsa.

legit latest news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Najeriya na neman dala biliyan 25 na bututun iskar gas zuwa Turai

Najeriya na neman dala biliyan 25 a matsayin kuɗin...

‘Yan sa-kai biyu ne suka mutu a harin da muka kai Zamfara – Sojoji

Rundunar sojin sama ta Najeirya ta tabbatar da kai...

Dakarun sojin ruwa a Najeriya sun yi kaɗan wajen tsaron ƙasa – Emmanuel Ogalla

Babban hafsan sojin ruwa na Najeriya ya ce dakarunsa...

Juma’a da Litinin ranakun hutun Sallar Layya – Gwamnati

Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun Juma'a da Liitnin masu...

Gwamnatin Neja zai haɗa kai da matatar Ɗangote wajen haƙo ɗanyen man fetur

Gwamnan jihar Neja, Umar Bago, ya nemi aikin haɗin...

Tchiani ya zargi Najeriya, Faransa, China da Amurka wajen cutar da Nijar

Shugaban sojin Nijar, Janar Abdourahmane Tchiani, ya zargi Najeriya...

An ceto yara 12 da aka yi safararsu a jihar Abia

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta ce jami'anta sun samu...

A na neman kusan Mutane 400 da suka ɓace a ambaliyar Neja

A na ci gaba da ayyukan ceto bayan ambaliyar...

Mun bayar da hutu ranar Litinin bisa jimamin mutuwar ƴan Wasa – Gwamnatin Kano

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya ayyana ranar...

Tun farko na shaida wa Tinubu ba zan zaɓe shi ba – Amaechi

Tsohon ministan sufuri na Najeriya, Rotimi Amaechi ya ce...

Fernandes na duba yiwuwar barin Man Utd zuwa Al-Hilal

Bruno Fernandes na duba yiwuwar ficewa daga Manchester United...
X whatsapp