Super Eagles dai na ci gaba da makale wa a filin tashi da saukar jiragen sama na Al Abaq sa’o’i 12 da sauka a kasar Libya.
Jirgin na ValueJet da aka yi hayar ya kasance abin ban mamaki kuma cikin haɗari, an karkatar da shi zuwa ƙaramin filin jirgin sama daga Benghazi a daidai lokacin da matukin jirgin ke kammala tunkarar filin jirgin Benghazi a daren Lahadi.
Hukumar kwallon kafa ta Lbyan ta gaza aikewa da wata tawagar karbar baki ko ma ababen hawa da za su kai tawagar daga filin jirgin zuwa otal din nasu, inda aka ce ana tafiyar sa’o’i 3 a Benghazi, kamar yadda hukumar kwallon kafar Najeriya NFF ta bayyana.
Hukumar ta NFF ta yi tanadin motoci daban-daban ga tawagar amma shirin ya ci tura saboda karkatar da jirgin.
‘Yan wasan sun yanke shawarar ba za su kara buga wasan ba yayin da jami’an NFF ke shirin tashi da kungiyar zuwa gida.
A ranar Talata ne Super Eagles za ta kara da Libya, bayan nasarar da suka yi a wasan farko da ci 1-0 a ranar Juma’ar da ta gabata.