‘Yan wasa 11 ne suka isa sansanin Super Eagles da ke Lisbon gabanin wasan sada zumuncin kasa da kasa da Portugal.
‘Yan wasan farko sune mataimakin kyaftin, William Troost-Ekong, Alex Iwobi, Joe Aribo da Ademola Lookman.
Sauran ‘yan wasan da ke sansanin su ne Bruno Onyemaechi da Kevin Akpoguma da Oghenekaro Etebo da Ebube Duru da Emmanuel Dennis Paul Onuachu da kuma Calvin Bassey.
Ana sa ran sauran ‘yan wasan 12 za su shiga takwarorinsu a ranar Talata.
Tuni dai babban kocin, Jose Peseiro ya gayyaci Cyriel Dessers da Chidozie Awaziem a matsayin wadanda za su maye gurbin Victor Osimhen da Olisa Ndah.
Kungiyar za ta yi atisayen farko a daren yau.
Za a fara atin ne da karfe 8 na dare agogon Najeriya.