Ma’aikatan agaji daga kasashen waje sun isa Moroko domin taimakawa takwarorinsu na kasar a aikin ceton wadanda girgizar kasa ta sanya suka makale a baraguzan gini ko tsaunukan da aka gagara isa.
Sama da mutane 2100 ne suka mutu a girgizar kasar ta daren Juma’a.
Gwamnatin Moroko ta ce ta amince da taimakon gaggawar da kasashen Qatar, da Hadaddiyar daular Larabawa da Birtaniya da Sufaniya suka yi.
Daruruwan mutane na ta turuwa asibitico domin bada taimakon jini a Marrakesh.
Manel Houda, ma’aikaciyar asibiti ta ce lamarin ya munana, amma suna baÆ™in kokarinsu.


