Tawagar gwamnatin Kano da Jigawa sun kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan Alhaji Aminu Ɗantata, wanda ya rasu yana da shekara 94.
A ranar Asabar ɗin da ta gabata ne shahararren ɗankasuwan ya rasu a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa bayan fama da jinya.
Tuni dai tawagar da gwamnatin Najeriya ta tura zuwa Madina ta isa ƙasar Saudiyya domin halartar jana’izar fitaccen attajirin.
A na sa ran a yau Talata, bayan sallar La’asar ne za a gudanar da jana’izarsa a masallacin Madina.