Tawagar Ecowas ta musamman da ta ziyarci Nijar, ta samu ganawa da shugabannin mulkin sojin ƙasar a wani yunƙuri na maido da hamɓararren shugaban ƙasar Mohamed Bazoum kan karagar mulkin ƙasar.
Tawagar masu shiga tsakanin ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban Najeriya, janar Abdulsalamu Abubakar mai ritaya da mai Alfarma sarkin Musulmin Najeriya Muhammad sa’adu Abubakar lll, ta samu ganawa da shugaban mulkin sojin kasar Janar Abdourahamane Tchiani.
Tawagar ta Ecowas ta kuma samu ganawa da hamɓararren shugaban ƙasar Mohamed Bazoum.
Ziyarar masu shiga tsakanin na zuwa ne kwana guda bayan da manyan hafsoshin tsaron ƙasashen Ecowas suka ce, sun saka ranar afka wa Nijar da yaƙi, matsawar sojojin ba su mayar da Bazoum kan mulki ba.
Sojojin mulkin sun tattauna da tawagar Ecowas ɗin a birnin Yamai, to sai dai ba su yi bayani abubuwan da suka tattauna ba.
Tattaunawar na zuwa ne a daidai lokacin da ake ɗaukar dubban ‘yan sa kai domin kare ƙasar daga farmakin Ecowas. In ji BBC.