Jam’iyyar New Nigerian Peoples Party, NNPP, ta ce tattaunawar kawancen jam’iyyar da jam’iyyar Labour (LP) tana tafiya cikin kwanciyar hankali.
A cewar jam’iyyar, dan takararta na shugaban kasa, Dr Rabiu Kwankwaso, na iya amincewa da zama abokin takarar Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP.
Ana ci gaba da rade-radin cewa, dukkanin ‘yan siyasar biyu na iya hadewa su kafa wata kafa mai karfi domin fafatawa da manyan jam’iyyun siyasar kasar nan, wato PDP, da kuma APC mai mulki.
Da aka nemi a tabbatar da batun kawancen, sakataren yada labarai na jam’iyyar NNPP na kasa, Dokta Agbo Major ya shaida wa Aminiya cewa har yanzu ana ci gaba da tattaunawa don haka ba zai so yin hasashe ba.
Sai dai ya bayyana cewa Kwankwaso ko Obi na iya amincewa da zama mataimakin juna.