Tattalin arzikin Najeriya ya haɓaka da kashi 3.46 a rubu’i na uku na shekarar 2024, daga kashi 3.19 a rubu’i na biyu na shekarar.
Babban bankin Kasa ne ya bayyana hakan a cikin rahotonsa, inda ya ƙara da cewa yawanci an samu cigaban ne daga wasu ɓangarorin daban da na albarkatun man fetur.
Rahoton ya kuma ce hauhawar farashin kayayyaki ya ragu a ɗan tsakankain.
A ɓangaren man fetur, rahoton ya ce man da ake fitarwa a Najeriya ya ƙaru zuwa ganga miliyan 1.33 a kullum, daga ganga 1.27 da ake fitarwa a rubu’i na biyu na shekarar, wanda rahoton ya ce bai rasa nasaba da tsaro da aka samu a yankin Neja Delta.
CBN ya ce haɓakar da ake samu na da nasaba ne da ƙoƙarin inganta harkokin kasuwanci a ƙasar.