fidelitybank

Tattalin arzikin Najeriya ya haɓaka sosai – Bankin Duniya

Date:

Bankin Duniya ya ce, tattalin arzikin Najeriya haɓɓaka fiye da kowanne lokaci cikin shekara goma da ta gabata, sakamakon wasu muhimman gyare-gyaren da gwamnati ta aiwatar sai dai kuma Bankin Duniyan ya gargadi cewa hauhawar farashin kayayyaki na ci gaba da addabar miliyoyin ƴan ƙasar.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Bankin Duniya ya fitar wa manema labarai, inda ya bayyana cewa ƙarfin tattalin arziƙin Najeriya na cikin gida ya ƙaru da kashi 4.6 cikin 100 a zangon ƙarshe na shekara ta 2024.

Wannan, in ji Bankin Duniya ya kai jimillar ci gaban tattalin arziki na shekara zuwa kashi 3.4 cikin 100 – mafi girma tun shekarar 2014, baya ga farfaɗowar da aka samu daga lokacin annobar korona.

Rahoton ya danganta wannan cigaba ne ga ci gaban da ake samu a ɓangaren man fetur da iskar gas, da kuma ƙaruwar zuba jari da bunƙasar fasahar zamani da harkar kudi.

“Duk da wannan ci gaba, ɓangaren noma ya ci gaba da tafiyar hawainiya, inda ya karu da kashi 1.2 cikin 100 kacal a shekarar 2024,” in ji Bankin.

Bankin ya kara da cewa, “Wannan ƙarancin ci gaba ya samo asali ne daga rashin tsaro a yankin tsakiyar ƙasar da aka fi yin noma, da kuma hauhawar farashin kayayyakin noma kamar taki da man fetur.”

“Wadannan kalubalen suna da tasiri kai tsaye ga samar da abinci da kuma hauhawar farashin kayan masarufi, wanda ke ƙara matsin rayuwa ga miliyoyin ‘yan Najeriya,” in ji rahoton.

Bankin Duniya ya yaba wa gwamnatin shugaban Bola Ahmed Tinubu saboda ɗaukar matakan gyaran tattalin arziki tun bayan hawansa mulki a watan Mayun 2023.

Daga cikin wadannan gyare-gyare har da cire tallafin man fetur da ƙoƙarin farfaɗo da darajar Naira. Sai dai kuma rahoton ya ce waɗannan matakan sun haifar da matsin rayuwa ga al’umma da dama, musamman talakawa

nnnnews

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...

Isra’ila ta gano gawar ƴan ƙasarta

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta gano gawar ''yan...

Ma’aikatan wutar lantarki a Abuja sun fusata

Ma'aikatar kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja Electricity Distribution...

Ƴan Najeriya 147 da suka maƙale a Nijar sun dawo gida

Gwamnatin Najeriya ta tarɓi 'yan ƙasar 147 aka kwaso...

Alhazai Miliyan Ɗaya da Rabi ke tsayuwar Arfa

Dubun dubatar alhazai daga sassan duniya na hawan Arafa...

Sarkin Kano na 15 ya dakatar da yin hawan Sallah

Mai martaba Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado...

Maniyacin jihar Kano da yake kokarin zama Alhaji ya rasu a Saudiyya

Daya daga cikin alhazan jihar Kano, Shu’aibu Jibrin, an...

Tinubu ya bayar da tallafin Biliyan Biyu da Tirela 20 na Shinkafa ga al’ummar Mokwa

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya ce, shugaban ƙasar...

Gwamna Adeleke na Osun ya gana da Tinubu

Gwamnan jihar Osun Ademola Adeleke ya kai ziyara ga...

An samu gawar mutane 7 a ambaliyar Neja

Rahotonni na cewa masu aikin ceto sun zaƙulo gawar...
X whatsapp