fidelitybank

Tasirin Najeriya na zubewa a Afrika – Obasanjo

Date:

Masana harkokin dfplomasiyya a Najeriya, sun fara tofa albarkacin bakinsu a kan wani furuci da tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya yi cewa, tasirin Najeriya a duniya yana raguwa, musamman ma a kan kasashen nahiyar Afirka.

Wasu masana na ganin cewa akwai gaskiya a cikin maganar, suna danganta lamarin da rashin ƙwararrun masu ba da shawara ga shugabanni da kuma rashin aiki da ita idan an ba su.

Tsohon shugaban, Cif Olusegun Obasanjo, ya yi wannan furucin ne a wajen wani bikin ƙaddamar da littafi a kansa, musamman ma yadda ya shahara wajen rubuta wa shugabannin Najeriya wasikar bankada ko tonun silili.

Ya ce tasirin kasar na fada a ji da kuma dadadden kallon da ake mata na babbar Yaya, kuma rumfa sha shirgi na ci gaba da raguwa musamman ma a kan kasashen nahiyar Afirka, sakamakon gazawa ko rashin tabuka abin kirki wajen jagorantar kannen nata.

Cif Obasanjon ya buga misali da wata gazawa da ya ce Najeriya ta yi wajen daidaita tsakanin shugabanni da ƴan tawaye a kasar Chadi – lamarin da sai da ƙasar Qatar ta dako gari daga nahiyar Asiya ta je ta shiga tsakani.

Tuni dai wasu masana huldar jakadanci suka fara tofa nasu albarkacin bakin a kan wannan maganar.

Ambasada Sulaiman Dahiru, tsohon jakadan Najeriya ne, wanda ya ce duk da cewa Cif Obasanjo kan ji babu wanda ya yi komai in ba shi ba…a wannan ɓigiren ya fadi gaskiya.

Sai dai na tambayi Ambasada Sulaiman Dahiru ko da wani abu da Najeriyar za ta yi don mai da martabar tata ta jagora ga kasashen nahiyar Afirkan?

A shekarun baya, an yi zamanin da Najeriya ta yi tasiri a kan kasashen Afirka da wasu kasashen duniya, musamman irin rawar da ta taka wajen yaki da nuna launin fata a kasar Afirka ta kudu da wasu makwabtanta.

Akwai ma lokacin da kasa irin Amurka ba ta daukar wani mataki a kan Afirka sai ta nemi shawarar Najeriya.

sani ahmad

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Kotu ta ɗaure Matashin da ya shiga ɗakin kwanan Ɗalibai Mata a Kano

Babbar Kotun Shariʼar Musulunci da ke Kofar Kudu a...

Ban gudu daga PDP ba – Namadi Sambo

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Mohammed Namadi Sambo, ya ƙaryata...

Da yuwar Sojojin mu za su shiga yaƙi don tallafa wa Isra’ila – Trump

Rundunar sojin Isra'ila IDF ta ce ta ƙaddamar da...

Isra’ila ta kai hari cibiyoyin ƙera nukiliyar Iran

Yayin da aka shiga rana ta shida na yaƙi...

Najeriya za ta kwashe ƴan ƙasarta dake zaune a Iran da Isra’ila

Gwamnatin tarayya ta ce, tana kammala shirye-shiryen gaggawa domin...

Makami mai Linzami ya faɗa kan cibiyar tattara bayanan sirrin Isra’ila

Kafar yaɗa labarai ta gwamnatin Iran ta ce, ƙasar...

Iran ta ƙaddamar da sabbin hare-haren makamai masu linzami kan Isra’ila

Rundunar sojin Isra'ila ta ce, Iran ta ƙaddamar da...

Isra’ila ta na da makaman nukiliya 90

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya dade yana cewa Iran...

Kashe jagoran Iran Ayatullah shi ne kawo ƙarshen rikici – Isra’ila

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce duk wani shiri...

Jerin sunayen masu Fashin Waya 51 da aka kama a Kano

Rundunar ƴansandan Kano, ta fitar da jerin sunayen Mutane...

Iran ta dakatar da tashin jirgi a ƙasarta

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Iran ta...

Poland za ta kwashe dukkannin ƴan ƙasarta daga Isra’ila

Poland na shirin kwashe kusan ‘yan kasarta 200 daga...
X whatsapp