Mazauna karamar hukumar Mangu da ke jihar Filato sun shiga tashin hankali, bayan sace wani Basarake.
Jaridar Punch ta rawaito cewa, ‘yan bindiga sun sace mai martaba, Diket Gupiya a Mangu.
Mai martaba Diket Gupiya shi ne mai rike da kasar Pushit. Daga wannan yanki a garin Mangu ne mataimakin gwamnan jihar Filato watau Sonny Tyoden ya fito.
Ana zargin wadannan ‘yan bindiga sun dauke Sarkin Pushit a fadarsa da ke kauyen Pushit a cikin daren ranar Alhamis din ta wuce, 24 ga watan Fubrairu 2022.