Akalla mutane 12 ne suka kone kurmus a wani hatsarin mota da ya afku a garin Tsamawa da ke karamar hukumar Garun Malam a jihar Kano.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar, SFS Saminu Abdullahi ya raba wa manema labarai a ranar Talata.
Ya ce, “Mun samu kira daga wani Isah Mai-Fetur da misalin karfe 3:00 na rana cewa, wata motar bas ta Hiace da wata motar bas J5 sun yi karo wuta nan take ta kama. ,Bayan samun labarin, mun aika da tawagar mu cikin gaggawa zuwa wurin da abin ya faru da misalin karfe 3:12 na rana domin ceto wadanda abin ya shafa,” in ji sanarwar.
Ya kuma ce, mutane 11 da ke cikin motar Hiace sun taho ne daga hanyar Zariya zuwa Kano, yayin da mutum daya a cikin motar J5-bus shi ma ya na zuwa Kano daga Zariya.
Abdullahi ya ce, dukkan mutanen 12 sun kone kurmus, kamar yadda ya ce, hatsarin ya faru ne da gudun wuce sa’a da su ka yi.
Ya kuma shawarci masu ababen hawa da su rinka tuka mota a hankali domin gujewa abubuwan da ba a zata ba.