Akalla mutane bakwai ne aka tabbatar da mutuwarsu, sakamakon gubar abinci a kauyen Danbaza da ke karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara.
Lamarin ya faru ne bayan ‘yan uwa sun ci Dambu, wanda aka shirya a matsayin abincin dare.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa, wadanda suka mutu, matan aure biyu da ‘ya’yansu biyar, sun mutu nan da nan bayan an gama cin abinci.
A cewar wani dan uwa, Alhaji Muhammad Kabir, da mutane suka gama cin abincin, hudu daga cikin wadanda suka mutu nan take, yayin da uku kuma aka garzaya da su asibiti inda likitoci suka tabbatar da cewa sun mutu.
“An zargi wadanda suka mutu da amfani da guba wajen dafa abincin,” in ji shi.
Tuni dai aka yi jana’izar mutanen bakwai da suka mutu a garinsu na Danbaza, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Shugaban karamar hukumar Maradun, Umar Mu’azu, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an aika wakilai daga karamar hukumar domin jajantawa iyalan mamatan.
Majalisar karamar hukumar ta bukaci ‘yan uwa da su karbi wannan rashi a matsayin iznin Allah tare da addu’ar Allah ya baiwa iyalan hakurin jure rashin.


