fidelitybank

Tashin Hankali: Mazauna Ukraine sun shiga firgici

Date:

Mazauna birnin Kyiv a kasar Ukraine sun shiga cikin firgici tare da jin ƙarar fashe-fashe da kuma jiniya da ke ta tashi a kasar.

Tuni mazauna birnin ke neman wajen mafaka a tashoshin jirgin ƙasa, suna kuma layi a wuraren cirar kuɗi na banki, da gidajen mai da manyan kantunan sayar da kayan masarufi.

Yayin da ‘yan Ukraine ɗin suka wayi gari da abin da suka daɗe suna jin tsoro na harin na Rasha, can kuma a wasu sassan kasar, cuncurundon ababan hawa ne ake gani na waɗanda suke kokarin ficewa.

Mai magana da yawun fadar shugaban ƙasar, ya ce Rasha na so ta ribaci firgicin da ta jefa fararen hula ne kawai, yana mai shawartar jama’a da kada su karaya.

To amma wannan ga alama bai kwantar da hankali ba, domin tuni wasu ‘yan kasar suka fara tsallaka iyakar ƙasar ta kudu maso yamma zuwa cikin Romania domin samun mafaka.

Ita ma Poland tuni ta samar da wurare takwas na karbar mutane, ko da za a fara neman tsira, inda za ta samar da abinci da kula da lafiya da kuma samar da bayanai.

assu today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp