Wani abin fashewa da ake kyautata zaton Bam ne ya kashe mutum biyu a wata matatar man fetur da ke garin Izombe na Jihar Imo a yau Laraba, a cewar rahoton kafar talabijin ta Channels TV.
Rahoton ya ce, fashewar ta afku ne da sanyin safiya a ma’aikatar da ke ƙarƙashin kulawar kamfanin Addax Petroleum Development Nigeria Limited.
Kakakin ‘yan sandan Imo, Micheal Abattam, ya tabbatar da mutuwar mutanen ga Channels, yana mai cewa, rundunar ta tura jami’anta masu kwance Bam.
Wani da lamarin ya faru a kan idonsa ya faɗa wa Channels cewa mutanen da suka mutun su ne ke ɗauke da bam ɗin.
Ya ƙara da cewa, bam ɗin ya fashe ne yayin da mutanen ke ynƙurin shiga da shi farfajiyar wurin