fidelitybank

Taron kolin ECOWAS: Osibanjo ya nufi kasar Ghana

Date:

A yau ne mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo zai tafi birnin Accra na kasar Ghana domin wakilcin Najeriya a wani babban taron koli na kungiyar ECOWAS kan harkokin siyasa a kasar Mali da sauran sassan yankin.

Wata sanarwa da babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, Laolu Akande ya fitar, ta ce, a wajen taron, Osinbajo zai bi sahun sauran shugabannin kasashen Yammacin Afirka, domin duba irin ci gaban da gwamnatin mulkin sojan Mali ta samu kan komawar kasar bisa tafarkin dimokuradiyya.

Taron zai karba tare da yin la’akari da sabon rahoto daga mai shiga tsakani na ECOWAS a Mali, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, wanda ya ziyarci Bamako tsakanin 18 zuwa 20 ga watan Maris domin ganawa da shugaban mulkin soja. Shugabannin kasashen za su kuma duba halin da ake ciki a Jamhuriyar Burkina Faso da Guinea.

Bayan da sojoji suka kwace iko da gwamnatoci a Mali, Guinea da Burkina Faso, tare da kakaba takunkumi kan gwamnatin mulkin soja a wadannan kasashe, shugabannin ECOWAS a taron da suka yi na karshe a watan Fabrairu sun tabbatar da cewa gwamnatocin demokradiyya ne kadai za a amince da su tare da tallafawa a yammacin Afirka.

legitnew

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp