An haifi Abdullahi Umar a ƙauyen Ganduje da ke cikin ƙaramar hukumar Dawakin Tofa ta jihar Kano a 1949.
Ya fara karatun Ƙur’ani da Islamiyya a ƙauyensu, inda ya samu ilimin addini. Ya shiga firamare ta Dawakin Tofa daga 1956 zuwa 1963.
Ganduje ya fara makarantar sakandiren Birnin Kudu a 1964 inda ya kammala a 1968.
Ya shiga makarantar horar da malamai da ke Kano tsakanin 1969 zuwa 1972.
Tsohon gwamnan jihar Kanon ya samu digirinsa na farko a fannin ilmin malanta a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria cikin jihar Kaduna a 1975.
A 1979 ne kuma ya kammala digirinsa na biyu a Jami’ar Bayero ta Kano, sannan ya sake komawa Jami’ar Ahmadu Bello daga 1984 zuwa 1985 don karanta fannin gudanar da harkokin gwamnati.
A 1993 ne ya samu digirin-digirgir daga Jami’ar Ibadan. In ji BBC.