A ranar Alhamis ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya mayar da martani kan rasuwar Hajiya Ladi Bako, matar Audu Bako, marigayi Gwamnan Soja na jihar Kano.
Buhari ya bi sahun ‘yan uwa da abokan arziki da gwamnati da al’ummar jihohin Kano da Jigawa wajen alhinin rasuwar Ladi Bako, wadda ta kasance daya daga cikin mata masu karfin fada aji a lokacinta.
Garba Shehu, babban mataimaki na musamman ga shugaban kasar ne ya bayyana hakan.
Buhari ya kuma ce, za a rika tunawa da marigayiyar, bisa amincinta ga al’ummar Kano.
A cikin karramawar, Buhari ya ce: “Marigayi Hajiya Ladi ta kasance babbar mace. Ta ayyana wani zamani da za a dinga tunawa da ita don amincinta ga danginta da al’ummar Kano.
“Allah ya ba wa wadanda ta bari a baya da karfin gwiwa da juriya don daukar wannan rashi mara misaltuwa.”