Kungiyar tsofaffin ‘yan wasan Super Eagles a karshen mako, sun kai ziyarar ban girma ga dan takarar shugaban kasa, kuma jagoran jam’iyyar (APC) na kasa, Bola Ahmed Tinubu.
A cikin wani faifan bidiyo da aka yada ta yanar gizo, an ga Fasto Taribo West na fadin albarkacin bakinsa a wajen taron neman takarar shugaban kasa na 2023 na Tinubu.
Tsohon dan wasan na Super Eagles ya yi addu’ar Allah ya mayar da Najeriya a matsayin ta ta hannun Tinubu.
Sauran fitattun jiga-jigan ‘yan wasan kwallon kafa na Najeriya da suka halarta akwai Austiin ‘Jay Jay’ Okocha da Kanu Nwankwo, da kuma Victor Ikpeama da Peter Rufai.
Tinubu wanda ke cika shekaru 70 a wannan watan, ya bayyana kudirinsa na tsayawa takarar shugaban kasa gabanin zaben 2023, kuma akwai shirye-shiryen daukar wani sabon salo na karrama shi.
Haka ma dai wasu daga cikin ‘yan wasan sun kai wa Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi ziyara a shekarar da ta gabata gabanin wani sabon wasa da aka yi tsakanin ‘yan majalisar zartaswa na jihar da na 1994 da 1996 na tsohon Super Eagles a filin wasa na Confluence dake Lokoja. babban birnin jihar.
A wancan lokacin, an yi ta yada jita-jitar cewa Gwamnan Kogi na shirin tsayawa takarar shugabancin Najeriya a 2023.
Taribo West, wanda ya zakaran UEFA Cup tare da Inter Milan ya zama Fasto bayan kammala kwallon kafa.