Wani mai sharhi kan al’amuran jama’a, Durojaiye Ogunsanya, ya shiga cikin cece-kucen da ke tattare da takardar shaidar shugaban kasa Bola Tinubu daga jami’ar jihar Chicago ta kasar Amurika.
Tun a baya ne ake ta cece-ku-ce kan sahihancin shugaba Tinubu, musamman a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyun adawa da ke neman lalubo hanyar da za a bi domin ganin shugaban ya sauka daga mulki.
Wani sashe na ‘yan Najeriya na ta mamakin dalilin da ya sa tsohon gwamnan jihar Legas ba zai iya nuna kowa a matsayin abokin karatunsa ba yayin da yake makarantar.
Shi ma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya garzaya wata kotu a Amurka, inda ya nemi a ba shi takardar shaidar Tinubu a jami’ar Chicago.
Sai dai kuma a cewar wani faifan bidiyo da ke zagayawa a shafukan sada zumunta, Ogunsanya yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na TVC ya tabbatar da cewa shugaban da kansa sun kammala karatun jami’a a shekarar 1979.
Ya ce, “Mun hadu a makarantar, Jami’ar Jihar Chicago, kuma muna sashen guda daya, College of Accounting Business and Administrative, muna da digiri a fannin Accounting, kuma muna aji daya tare kuma muka kammala.
“Ya halarci Jami’ar kuma ya kammala a shekarar 1979 a shekarar da na yi. Na zo nan ne don shaida cewa ya halarci Jami’a kuma ya kasance ƙwararren dalibi.
“Ina nan da Diploma na, domin duniya ta gani. Mun kammala karatunmu tare a jami’a, kawai ina so in kafa tarihi ba don wata riba ko wata alfarma ba”.


