Yayin da Najeriya ke shirin gudanar da babban zaɓe a 2023, ƙungiyar Tarayyar Turai (EU) ta bayyana goyon bayanta ga ƙasar don gudanar da sahihin zaɓe.
Da take magana a ziyarar da ta kai Jihar Edo, Jakadan EU a Najeriya Samuela Isopi, ta ce ci gaban Najeriya na da muhimmanci gare ta a matsayin ƙawa.
“Yau saura kwana 70 kafin gudanar da zaɓuka, saboda haka ne muke son yin amfani da ziyararmu wajen ganawa da ‘yan siyasa don tattauna lamurran zaɓe,” in ji ta.
“EU ta sha tallafa wa harkokin zaɓe a Najeriya tun lokacin da ta koma turbar dimokuraɗiyya. Mun turo masu saka ido da yawa kuma za mu sake yin hakan a zaɓe mai zuwa.”