Ƙungiyar Tarayyar Turai ta amince da ƙaƙaba wa Rasha ƙarin takunkumai saboda yaƙin da take yi da Ukraine.
Sabbin takunkuman sun shafi fannonin kuɗi da makamashin ƙasar.
Ƙungiyar ta amince ta ƙaddaye farashin man fetur na Rasha kan sama da dala 40 kawai kan kowace ganga.
Shugabar hukumar gudanarwar ƙungiyar, Ursula von der Leyen, ta ce EU ƙoƙarin gurgunta babban abin da Rasha ta dogara da shi a yaƙin.
Ministan harkokin wajen Faransa, Jean-Noel Barrot za su yi abin da zai tilasta wa Rasha tsagaita wuta ba tare da amfani da ƙarfi ba.
Shugaban Ukraine, Volodymir Zelensky ya yaba wa sabbin takunkuman waɗanda ya kira ”masu muhimmanci da aka aitawar a lokacin da ya dace”.